Gwmanatin Sojin Nijar ta sanar da cewa sun sasanta da Gwmanatin Najeriya.
Hakan ta faru ne bayan ziyarar aiki da Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ya kai birnin Yamai, fadar gwamnatin Nijar.

Bayan sanya hannu kan takardar, Ministan Harkokin Wajen Nijar, Bakary You Sangare, ya bayyana cewa, “da ma Najeriya ’yan uwanmu ne, duk wanda ya ce zai raba Nijar da Najeriya, shi da kansa ya san ba gaskiya yake ba, abu ne na Allah. Allah Ne Ya haɗa wannan zumunta ka, babu wanda ya isa ya raba ta.”
Hukumar tace finafinai za ta fara kamen yan adaidaita sahu a Kano
Takwaransa na Najeriya, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa nan gaba Shugaba Bola Ahmed Tinubu za su gana da shugaban gwamnatin sojin Nijar, Janar Abdurrahman Tchiani, a matsayin ci gaban wannan daidaitawa.
Ya bayyana cewa yarjejeniyar da ƙasashen biyu su ka sanya hannu a kai, ta zama, “darasi ga duk wasu ƙasashen duniya, domin yanzu an shiga wani lokaci da ake fama da tashe tashen hankali. To yanzu mu abin da a muka a tsakaninmu ya zama abin koyi.”
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito danganta tsakanin gwamnatin Nigeria da ya mulki soji dake Nijar ta yi tsami ne tun lokacin da aka hambarar da gwamnatin Bazum wacce gwamnati ce ta dimokaradiyya.