Fadar shugaban Najeriya ta nesanta kanta daga wasu allunan tallar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima na zaɓen shekarar 2027.
Mai magana da yawun shugaban Bayo Onanuga yace babu hannun fadar shugaban ƙasar dangane da waɗannan talla da suka mamaye biranen Abuja da Kano.

Onanuga ya ce shugaba Tinubu da mataimakinsa Kashim sun gamsu da irin goyan bayan da suke samu, amma kuma basa so ayi riga malam Masallachi, wajen fara yakin neman zabe tun lokacinsa bai yi ba.
Fadar shugaban ƙasar tace dokar zabe ta haramta duk wani yaƙin neman zabe ba bisa ƙa’ida ba, saboda haka suna kira ga magoya bayan su da su mutunta ta.