Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Jaridar Vanguard ta Karrama Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano da lambar yabo ta gwamnan da ya fi kowanne gwamma iya shugabanci a Shekarar 2024 bisa la’akari da irin nasarorin da ya samu a bangaren ilimi da kiwon lafiya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24 ranar Asabar.
Gwamna Yusuf ya karbi lambar yabon ne a wani gagarumin biki da aka gudanar a Legas, inda aka karrama fitattun mutane daga sassan kasar nan da suka yi fice a harkar shugabanci da hidimtawa al’umma.

Da yake jawabi a wajen bikin, Shugaban bikin, Atedo Peterside, ya jaddada cewa, an zabi wadanda aka karrama din ne bisa cancanta, kuma ya yaba wa wadanda aka karrama din bisa irin gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban kasa.
Babban Editan jaridar Vanguard, Eze Anaba, ya yabawa Gwamna Yusuf bisa yadda ya samar da kyakkyawan tsarin mulki ta hanyar jajircewarsa, da mayar da hankali kan manufofin da suka shafi jama’a.
Musa Iliyasu Kwankwaso, Rabi’u Sulaiman Bichi sun kama aikin da Tinubu ya ba su
A nasa jawabin, Gwamna Yusuf ya nuna jin dadinsa ga jaridar Vanguard bisa karramawar da ta yi masa, inda ya sadaukar da karramawar ga al’ummar jihar Kano.
Ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da tallafawa al’ummarsa da samar da ababen more rayuwa don jin dadi da walwalar al’ummar jihar Kano.
Sauran wadanda aka karrama a yayin taron sun hada da Gwamna Umar Namadi (Jigawa), Charles Soludo (Anambra), Douye Diri (Bayelsa), Biodun Oyebanji (Ekiti), Sheriff Oborevwori (Delta) da Hope Uzodinma (Imo).
Gwamna Yusuf ya samu rakiyar ‘yan majalisar zartarwa ta jiha, ‘yan majalisar dokokin jihar, masu ba da shawara na musamman, da shugabannin kananan hukumomi, da makusantan ‘yan siyasa.
Wannan karramawa ta zo ne kwanaki hudu bayan ya karbi lambar yabo ta Gwarzon Gwamnan da ya fi kowanne gwamma inganta ilimi a jiharsa wanda Jaridar Leadership.
Haka kuma gwamnan zai kuma karbi lambar yabo ta shugabanci nagari na Afirka daga Mujallar Heritage Times a karshen wannan watan a kasar Morocco.