Buba Galadima, jigo a jam’iyyar NNPP kuma Jagora a cikin tafiyar Kwankwasiyya, ya bayyana yadda ‘yarsa ta samu aiki a Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Najeriya (NUPRC) ta hannun Shugaba Bola Tinubu.
Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a gidan talabijin na AIT.
Galadima ya ce duk da sukar gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki akai-akai da ya ke yi, har yanzu shi aboki ne ga Shugaba Tinubu.
Tinubu ne ya Gyara min Gidana na Kaduna – Buhari
Ya ce: “Abokai ne mu kuma za mu ci gaba da kasancewa abokai. Idan ina da bukata daga gare shi, zan iya tambaya. Bari in bayyana a gaban al’umma. ‘Yata ta yi amfani da wayata ta kira Shugaban kasa, kuma ya dauka yana tunanin ni ne. Sai suka ce sun kira shi ne saboda rayuwa ta yi tsauri a kasar nan.

“Suka ce masa ‘Mahaifinmu ba zai iya yi mana wannan ba, amma ya fada mana kai abokinsa ne.’
“Karama daga cikinsu ta ce ta kammala hidimar kasa (NYSC), amma ta kasa samun aiki a Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta ta Najeriya (NUPRC) karkashin jagorancin Gbenga Komolafe. Tinubu kawai, ya kira Komolafe, ya ce ‘je ka ba ‘yar abokina aiki’. Shi ya sa take so ta je Makka domin godewa Allah da kuma godiya ga Shugaban kasa.”