Gwamnan Kano Abba Kabir Yusif ya tura wata tawaga ta musamman zuwa jihar Edo, domin binciken gaskiyar abin da ya faru na kisan gillar da akayiwa mafarauta ƴan asalin Kano a jihar.
An kafa kwamitin tawagar ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo.
Wata sanarwar da mai magana da yawun mataimakin gwamnan Ibrahim Garba Shu’aibu, ya fitar, ya ce kwamitin ya ƙunshi fitattun mutane daga Kano wanda suka haɗar da Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Isa Umar, Kwamishinan harkokin addini, shugaban ƙaramar hukumar Bunkure, Kwamishinar mata, kwamishinan ayyuka na musamman da sauran manyan jami’an gwamnatin Kano.
Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria
An dai kafa kwamitin ne domin binciken kisan Hausawa mafarauta ƴan asalin jihar Kano su 16 a garin Uromi na jihar Edo, wanda wasu matasa suka aikata mummunan kisan gillar ga Hausawan.

Mataimakin gwamnan Kano, ya bayyana cewa zasu yi bakin ƙoƙari wajen tabbatar da adalci ga iyalan waɗanda aka kashe.