Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Matatar man Ɗangote ta sanar da rage farashin litar man fetur da take siyar wa ƴan kasuwa masu gidajen mai zuwa naira 865 daga naira 880.
Idan za a iya tunawa a Wannan makon ne majalisar zartarwa ta kasa karkashin jagorancin Shugaban Kasa Bola Tinubu ta amine da sayar da danyen man ga matatun mai na cikin gida akan farashin naira.
Kadaura24 ta rawaito wata majiya ce daga matatar ta tabbatar wa da gidan talabijin na Channels hakan, inda ta ce an rage farashin ne a yau Alhamis.
Ragin farashin ya zo ne bayan wata tattaunawa da aka yi tsakanin matatar Ɗangote da ministan kuɗin Najeriya, Wale Edun a ranar Talata.
Dakatar da Umara: kungiyar kare hakkin dan adam ta Alhakku ta rubutawa Masarautar Saudia Wasika
Bayan taron ne gwamnatin Najeriya ta ce yarjejeniyar siyar wa Dangote ɗanyen mai da naira na nan, kuma za’a ci-gaba da amfani da ita duk da a baya kamfanin NNPCL ya sanar da kawo ƙarshen yarjejeniyar.

Da wannan matakin ne ake sa ran gidajen man fetur da suke da yarjejeniya da matatar Dangote irin su MRS da Ardova da Heyden da sauransu za su rage farashin litar man fetur ɗinsu.