Dakatar da Umara: kungiyar kare hakkin dan adam ta Alhakku ta rubutawa Masarautar Saudia Wasika

Date:

Daga Buhari Ali Abdullahi

 

Wata kungiya Kare hakkin dan adam mai suna Alhakku Human Rights and Social Justice organization ta bukaci hukumomin kasar saudiya da su janye dakatar da aikin ibadar Umrah da suka yi gabanin fara aikin hajjin bana.

Hakan na kunshe ne cikin wata Wasika da kungiyar ta rubuta sarkin Saudiya king Salman da mai kula da masallatan Harami, wadda shugaban kungiyar Saeed Bin Usman ya sanyawa hannu kuma aka aikowa Kadaura24.

InShot 20250309 102403344

Wasikar ta ce tabbas ta fahimci dalilan da su ka sanya hukumomin kasa mai tsarkin suka dakatar da ba da izinin shiga kasar, amma sun ce matakin zai takurawa mutane da dama don haka suke gani ya kamata a janye matakin.

” Muna yabawa da yadda ake dawainiya da masallatan Haramin Makka da Madina kuma mun san an dauki wannan matakin ne saboda gabatowar aikin Hajjin bana, amma muna nema a janye matakin dakatar da ba da izinin shiga kasar saboda matsalolin da hakan zai haifar”.

Yadda Tinubu ya taimakawa ‘yata ta sami aiki a hukumar kula da harkokin Man Fetur – Buba Galadima

“Muna fatan za a yi duba da dalilan na addinin musulunci da kuma na kasa da kasa da tausayawa dan Adam, wajen janye wannan matakin da muke da yakinin idan an janye shi al’umma da dama daga ko Ina a duniya za su ji dadin sa”. Inji Wasikar

Wasikar ta ce dakatar da ba da Visa zai cutar da tsofaffin da ba lallai su yi tsohon ran da za su yi Umara daga bayan ba, haka kuma dakatar da ba da izinin shiga kasar zai iya raba mata da kananan yara da suke son shiga kasar a tare kuma a lokaci guda.

Kazalika, matakin za iya hana wanda ya musulunta shiga kasar domin yin ibada cikin sauri.

FB IMG 1744283415267
Talla

Wasikar ta baiwa hukumomin kasar saudiyya wasu shawarwari kamar haka:

1. Inganta hanyoyin yin visa da tantance wadanda za su shiga kasar.

2. Inganta bibiya da bincikar wasu Shiga kasar har masaukansu don tabbatar da suna bin dokoki da ka’idojin kasar.

3. Inganta hanyoyin wayar da kan al’umma game da dokoki da ka’idojin kasar ta saudiyya.

Sun shawarci masarautar kasar ta saudiyya da ta samar da wani kwamiti a karkashin ma’aikatar aikin Hajji da Umara ta kasar domin bibiyar dokoki da ka’idojin kasar da kuma bullo da sabbin tsare-tsaren da za su yi daidai da kudirin kasar na vision 2030 .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu Yanzu: Hukumar KNUPDA ta rushe gaban shagon jarumar Tiktok Rahama

Daga Rahama Umar Kwaru   Hukumar KNUPDA ta kaddamar da rushe...

Wata kungiya ta bukaci Gwamnan Kano ya dakatar da Shugaban karamar hukumar Gwale

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Wata kungiya mai zaman kanta mai...

Kwankwaso ba zai koma APC ba – Buba Galadima

Kusa a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya karyata jita-jitar...

Yadda gwamnan Kano ya ke rabon kujerun aikin hajjin bana kamar gyada

Daga Rahama Umar Kwaru Al'ummar jihar Kano na cigaba da...