Daga Abdullahi Aliyu
Kungiyar ma’aikatan Radio talabijin da al’adu da wasannin gargajiya ta kasa reshen jihar kano (RATTAWU) ta kaddamar da rabon tallafin tagomashin kayan miyar sallah a Karo na Biyu ga ya’yan Kungiyar da iyalan yan kungiyar da su ka rasu.
Da yake jawabi Shugaban kungiyar kwamared Babangida Mamuda Biyamusu ya ce sun sauya tsarin daga shan ruwa a kowacce shekara zuwa bada tallafin kayan miyar sallah domin samar da walwala ga iyalan ‘ya’yan Kungiyar.

Kwamared Babangida Mahmud ya kuma roki Gwamnatin Jihar da ta taimaka domin samawa Kungiyar ofis na din-din-din don cigaban Kungiyar da ‘ya’yanta.
Ya bayyana kudirinsu na sake farfado da kimar kungiyar musamman saboda muhimmancin da ta ke da shi a harkokin yada labarai.
Karin haske kan dalilan yansanda na hana Hawan Sallah a Kano
A jawabinsa Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya yace a daukeshi Dan Kungiyar Rattawu tare da bada tabbacin samawa Kungiyar Muhalli na din din din bisa sahalewar gwamana.
Daga nan yace a madadin Gwamna zai bada gudunmawar Naira miliyan daya Domin walwalar yayan kungiya.
Karshe Kwamishinan yayi fatan Zaman lafiya da Hadin Kai ga kungiyar dama kasa Baki daya.