SANARWA !!!
kasancewar ranar Asabar, 29 ga watan Maris, 2025, za ta kasance jajiberin Ƙaramar Sallah, Ma’aikatar muhalli ta jihar Kano ta sauƙaƙa wa jama’a, don haka ma’aikatar ta baiwa al’umma damar fita don ci gaba da shirye-shiryen Sallah. Duk da haka, muna kira ga jama’a da su tsaftace muhallinsu, domin mu gudanar da bukukuwan Sallah cikin yanayi mai tsafta da kwanciyar hankali, sannan kuma sanitation na kasuwanni da ma’aikatu zai kasance kamar yadda a saba a gobe juma’a.

Allah Ubangiji ya ƙarbi ibadarmu, ya kuma zaunar da Jihar Kano lafiya.
Sanarwa daga Dr. Dahir M. Hashim
Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi
Jihar Kano