Hukumar Shari’ah ta jihar Kano ta rabauta da Bohal na sama da miliyan 10 daga kungiyar Wamy

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Hukumar Shari’ah ta rabauta da Katafaren Bohal na sama da Naira Miliyan 10 daga kungiyar World Assembly of Muslim Youth (Wamy) wanda aka ƙaddamar a harabar hukumar yau Alhamis .

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mukaddashin daraktan wayar da kai na hukumar shari’a Musa A Ibrahim (Best Seller) ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.

Sheikh Ali Danabba da yake bayani a madadin shugaban hukumar yace dole na su kara godewa Allah sannan mu godewa Kungiyar [WAMY] da suka gudanar da wannan gagarumin aiki na sadakatujjariya a wannan hukumar.

InShot 20250309 102403344
Talla

Dan Abba yace samar da rijiya mai sama da mita 150 abu ne mai dadi, wanda duk wanda yazo wannan gida a baya razana yake amma wannan ƙungiya suka yi namijin kokari wajen samar da ruwan akan kuɗi sama Naira miliyan 10.

Shugaban hukumar Sheikh Abbas Abubakar Daneji ya yi fatan alheri ga wannan ƙungiya duba da irin yadda suka maida hankali wajen kyautatawa wannan hukumar ta Shari’a “Wannan ba zai zama wani abin mamaki da wannan kungiyar ba, domin idan kuka kula kusan irin aiki daya wannan kungiyar take yi da wannan hukumar” Ya kuma yi kira da sauran kungiyoyi da suyi koyi da ayyukan wannan kungiyar domin cigaban musulunci da musulmi.

Sanarwa ta Musamman Daga Gwamnatin Jihar Kano

Da yake nasa jawabin shugaban kungiyar Wamy Hisham Abdussalam yace duk lokacin da ya shigo wannan hukumar ko kuma ya ji sunanta wani farin ciki yake ji a zuciyarsa, don haka suka mai da kai wajen taimakawa wannan hukumar.

Ya kuma bayyana cewar kungiyar Wamy ta yi fice a ciki da wajen kasar nan domin ayyukan cigaban musulunci da musulmi ko ina suke.

Hukumar Shari’a da ke jihar Kano an kafa tane a shekarar 2003 ƙarƙashin jagorancin gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau, kuma ita wannan hukuma tana gudanar da ayyukan tane akan duk abinda ya shafi addinin musulunci a jihar.

Hukumar ta sami dawamamme gata a wajen Gwamna Ibrahim Shekarau a wancan lokacin, sai dai bayan gushewarsa hukumar ta zama kamar kufai sabida lalacewa ba gyara.

Sai dai a yanzu Allah ya arzurta jihar da Gwamna Abba Kabir Yusuf me kishin jihar da hukumar, wanda yayi hangen nesa wajen zakulo mata ingantattun shuwagabannin da zasu gudanar da ita masu kishin addini da aikin gidan. Don haka muke fatan Gwamna Abba zai fita Zakka wajen dawo da wannan hukumar hayyacinta kamar a farkon ta ko ma ta wuce haka

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hawan Sallah: Yansandan Kano sun gayyaci hadimin Sarki Sanusi II bayan mutuwar wani

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta...

Barka da Sallah: Gwamnan Kano ya bukaci yan jihar su rungumi zaman lafiya da adalci

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Sarki Aminu da Sarki Sanusi sun bukaci gwamnati ta hukunta duk masu hannu a kisan Mafarautan Kano a Edo

Daga Aliyu Danbala Gwarzo da Sani Idris maiwaya   Mai Martaba...

Murtala Sule Garo ya yiwa Kanawa Barka da Sallah

Ina taya daukacin al’ummar Musulmi maza da mata musamman...