Kwamishinan harkokin tsaro na jihar Kano Manjo Janaral Muhammad Inuwa Idiris mai ritaya, ya ajiye aikinsa.
Kwamishinan dai bai bayyana dalilansa na sauka daga mukamin ba a takardar ajiye aikin da ya miƙawa gwamnan ba.

Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ta ce gwamna Yusuf ya kaɗu da ajiye aikin da kwamishinan ya yi tare da gode masa kan gudunmawar da ya bayar.