Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ranar Talata, ta jingine matakin da ta dauka tun farko kan mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16.
Kotun daukaka kara, bayan da ta fahimci an mika bayanan shari’ar ga kotun koli, ta umurci dukkan wadanda su ke cikin karar da su dakata har zuwa lokacin sauraron karar da suka shigar a kotun koli.
A wani hukuncin da aka yanke a ranar Talatar da ta gabata da wasu alkalai uku karkashin jagorancin mai shari’a Biobele Abraham Georgewill, kotun ta amince da janye karar da gwamnatin jihar Kano ta shigar bayan ta mika bayanan daukaka kara ga kotun koli.

Lauyan gwamnatin jihar Kano, Barista Ibrahim Wangida, ya mika wa kotu sanarwar daukaka kara kan hukuncin da aka yanke ranar Juma’a, 14 ga Maris, 2025.
Barista Wangida ya shaida wa kotun cewa an kammala dukkan matakan da su ka dace na shari’a, ciki har da mika bayanan shari’ar ga kotun koli.
Mika bayanan shari’ar zuwa Kotun Koli ya dakatar da duk wani mataki na hukuncin Kotun Daukaka Kara na ranar 14 ga Maris, 20015.
Da dumi-dumi: Wani kwamishina a Kano ya ajiye mukaminsa
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito Mai shari’a Abang, a ranar Juma’a, 14 ga Maris, 2025, ya bayar da umarnin dakatar da aiwatar da hukuncin da ta yanke a baya wanda ya tabbatar da dawo da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16.
Alkalin ya kuma umurci dukkan bangarorin da kowa a tsaya a inda yake kamar yadda wata kotu ta ba da umarni a ranar 13/6/2024 a cikin kara mai lamba 13/6/2024. FHC/KN/CS/182/2024.
Da yake bai gamsu da hukuncin da Justice Abang ya yanke ba, lauyan gwamnatin jihar Kano, Wangida ya caccaki hukuncin da aka yanke ranar Juma’a 14 ga watan Maris, wanda ya ce an yi kura-kurai wandanda suka sabawa kundin tsarin mulkin Nigeria, ya kuma ce tuni suka daukaka kara kuma suka mika dukkanin bayanan shari’ar zuwa gaban kotun koli.
Da yake mayar da martani ga sanarwar da aka shigar, Lauyan wanda ya shigar da kara, Abdul Fagge SAN, wanda bai ki amincewa da bukatar dayan bangaren ba, ya shaida wa kotun cewa abun da suka yi bai sabawa kundin tsarin mulki.
Idan za’a iya kadaura24 gwamnatin jihar Kano ta mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano na 16 bisa ga dokar masarautar Kano ta 2024. Haka kuma dokar ta tabbatar da tsige Aminu Ado Bayero a matsayin sarki na 15 tare da sarakuna hudu masu daraja ta daya da tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya nada.
Sai dai Aminu Ado Bayero bai gamsu da matakin gwamnatin ba, inda ya koma gidan Sarki na Nassarawa kuma ya ke kalubalantar tsige shi da gwamnatin jihar ta yi ta hannun Alhaji Aminu Dan Agundi.