Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta sanar da mutuwar babban mai taimaka wa gwamnan jihar na musamman kan harkokin Rediyo Abdullahi Tanka Galadanchi.
A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na fadar gwamnatin, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce Abdullahi Tanka Galadanchi ya rasu ne a yau Laraba a asibitin koyarwa na Aminu Kano bayan gajeren rashin lafiya.

Sanarwar ta ce gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya bayyana kaɗuwarsa sakamakon mutuwar, inda ya bayyana Abdullahi Tanka a matsayin jajirtacce kuma wanda ya samar da gudunmawa masu muhimmanci a ɓangaren yaɗa labarai da sadarwa a gwamnatinsa.
Da dumi-dumi: Wani kwamishina a Kano ya ajiye mukaminsa
”Mutuwar Abdullahi Tanka Galadanchi babban rashi ne ga gwamnatinmu da ma alummar jihar Kano baki-ɗaya” in ji sanarwar.
A cikin sanarwar, gwamnan ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalai da kuma abokan aikinsa a wannan lokaci na bakin ciki.