Ra’ayi: Madalla da Alhaji Murtala Sule Garo mai kyauta da hannun Dama Hagu ba ta sani ba – Aminu Dahiru

Date:

Daga Aminu Dahiru Ahmad

 

Madalla da Commander Alhaji Murtala Sule Garo mai kyauta da hannun Dama Hagu ba ta sani ba

~Hakika yabon gwani ya zama dole

Cikin ‘yan kwanakinnan kusan kodayaushe idan ka hadu da yan uwa abokan gwagwarmaya a siyasa sai dai ka ji ana cewa “Don Allah a yiwa jagora Alhaji Murtala Sule Garo godiya”.

Abin bai bani mamaki ba duba da yadda taimako da bada gudummawa ga al’ummar musamman yayan jam’iyyar APC ya zama al’adar His Excellency Alhaji Murtala Sule Garo.

InShot 20250309 102403344
Talla

Dalilin wannan rubutun nawa shine saboda inaso domin kowa ya shaida mun isar da sakon godiyarsa da tamu godiyar baki daya da jinjina ga wannan bawan Allahn wanda rashin gwamnanti ko rashin mukami bai hana shi abinda ya saba na taimakon al’umma ba. Hasalima sai kara fadada abin yayi.

Mutane da dama sun mika sakon godiyar su wasu a rubuce wasu a baka da baka akan wani abin arziki da Commander Murtala Garo ya yi musu ba tare da bayyanawa duniya ba.

INEC ta karbi takardar neman yi wa Sanata Natasha kiranye

Cikin wannan wata mai alfarma, Alhaji Murtala Sule Garo ya tallafawa shugabannin jam’iyya a matakin kananan hukumomi 44 na wannan jiha tamu mai albarka, wadanda su ka hada da ciyamomi da sakatarori da ma’aji da shugabannin matasa da na mata.

Alhaji Murtala Sule Garo ya tallafawa forum na ‘yan majalisar jiha wanda ya kunshi kimanin mutane 40.

Haka zalika Commader ya tallafawa forum na tsofaffin shugabannin kananen hukumomi 44, tare da mataimakansu da sakatarorinsu wanda su ka yi aiki tare har izuwa shekarar 2023.

Sarki Aminu Ado Bayero ya fara daukar matakan gudanar da Hawan Sallah Karama a Kano

Forum na Kansiloli wanda su ka yi aiki tare da Alhaji Murtala Sule Garo shima ya amfana da wannan tsari.

‘Yan social media da ‘yan rediyo da matan jam’iyya da matasan jam’iyya da kuma ‘yan kungiyoyi da jagorori da daidaikun mutane da ya saba tallafawa duk shekara sun amfana da wannan tsarin.

Duk wannan namijin kokarin ya yi shi ne a sirrance ba tare da tara mutane ko dauko camera a nunawa duniya ba duk da yin hakan ba laifi ba ne amma shi ya zabi yayi nasa a sirrance kamar yadda ya saba.

Kamar yadda annabin tsira ya ce, “Wanda Baya Godewa Mutane Ba Zai Godewa Allah Ba”.

Tabbas abin alfahari ne ga kowacce al’umma ta samu shugaba wanda kullum burinsa shi ne jibintar lamuran ‘ya’yanta.

Wannan ya sa naga ya dace amadadin jagoriri dukkan ‘yan jam’iyyar APC dake fadin jihar Kano na mika sakon godiya ga His Excellency, Alhaji Murtala Sule Galadima Garo bisa tallafin watan Azumin Ramadana da ya bawa dukkan azuzuwan mutanan da na ambata a sama.

Muna addu’ar Allah ya shiga lamuransa, ya kuma biya masa bukatunsa, ya saka masa da alkairi, Amin.

Haka zalika ina kira ga ‘yan jam’iyya da shauran al’ummar wannan jiha mai albarka da su ci gaba da sa wannan shugaba cikin addu’o’insu musamman a wannan watan mai alfarma domin Allah ya kara shiga lamarinsa ya kuma rikonda hannunsa. AMEEN

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hawan Sallah: Yansandan Kano sun gayyaci hadimin Sarki Sanusi II bayan mutuwar wani

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta...

Barka da Sallah: Gwamnan Kano ya bukaci yan jihar su rungumi zaman lafiya da adalci

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Sarki Aminu da Sarki Sanusi sun bukaci gwamnati ta hukunta duk masu hannu a kisan Mafarautan Kano a Edo

Daga Aliyu Danbala Gwarzo da Sani Idris maiwaya   Mai Martaba...

Murtala Sule Garo ya yiwa Kanawa Barka da Sallah

Ina taya daukacin al’ummar Musulmi maza da mata musamman...