Daga Isa Ahmad Getso
Sabon Hakimin Bichi da aka nada, Alhaji Munir Sanusi Bayero, ya ya kama aiki a hukumance, inda ya jaddada muba’arsa ga Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammadu Sanusi II tare da yin alkawarin yin adalci ga al’ummarsa
A jawabin da ya gabatar ga al’ummar garin Bichi, Wamban Kano ya bayyana tarihin yadda kakaninsa suka yi hakimcin garin Bichi da kuma alakar Bichi masarautar Kano.
Inda ya ce wasu daga cikin sarakunan Kano da suka shude da suka hada da Sarki Abdullahi Bayero da Khalifa Sir Muhammadu Sanusi duk sai da suka zama hakimai a Bichi sannan suka rike Sarautar Kano.

Alhaji Munir Sanusi Bayero ya bayyana matukar godiyarsa ga Sarki Muhammadu Sanusi II bisa yadda ya amince da shi har ya dora masa wannan nauyin. Ya bayyana godiya ga Sarki bisa irin goyon bayan da yake na shi goyon baya tun daga nada shi a matsayin Dan Maje har ya kai matsayin Wambai.

Ya kuma bukaci ‘ya’yan Masarautar da su ci gaba da ba da hadin kai da goyon bayan shugabancin Sarkin, inda ya jaddada cewa masarautar Dabo ta kowa ce. Ya yi gargadi game da rarrabuwar kawuna da kuma tasirin waje da ka iya kawo cikas ga daidaiton gidan sarauta.
Sarki Aminu Ado Bayero ya fara daukar matakan gudanar da Hawan Sallah Karama a Kano
A matsayinsa na Hakimin Bichi, ya yi alkawarin bin sahun magabatansa, musamman kaninsa, Wambai Abubakar, wajen ba da fifiko kan harkokin ilimi, da ayyukan yi, da walwala. Ya sha alwashin tabbatar da manufar Sarki Sanusi II, na bunkasa ilimi da tabbatar da samar da abinci mai gina jiki ga yara a yankin.
Wambai ya kuma mika godiyarsa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, tare da yaba masa bisa rawar da yake takawa wajen dawo da martabar Masarautar da kuma ciyar da ilimi gaba a jihar Kano. Ya yabawa shugabancin gwamnan tare da jaddada goyon bayansa ga ayyukan cigaban gwamnati a Bichi.