Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ɗauki ɗalibai 54 aiki bayan sun kammala karatun digiri na biyu a kan harkar kiwon lafiya a kasar waje.
Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ne ya baiyana hakan a wata sanarwa da ya aikowa Kadaura24.

Ya ce gwamnan ya sanar da bada guraben aikin ne a liyafar buɗe-baki da ya yi da daliban, wanda su ka dawo daga India bayan sun yi karatun na shekara ɗaya a jami’ar Symbiosis International University a Ranar Juma’a.
Ya ce tuni an kammala duk wasu tsare-tsare ga ɗaliban na su fara aiki a asibitocin gwamnati domin inganta harkar lafiya a jihar.
Sarki Aminu Ado Bayero ya fara daukar matakan gudanar da Hawan Sallah Karama a Kano
Ya kuma hore su da su yi amfani da ƙwarewar da su ka samo lokacin da su ke karatun a India a yayin gudanar da aiyukan su.