Kwankwaso ya soki Tinubu game da sanya dokar ta baci a jihar Rivers

Date:

Jagoran jam’iyyar adawa ta NNPP a Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki Shugaban Ƙasa Bola Tinubu game da dokar ta-ɓaci da ya saka a jihar Rivers da ke kudancin ƙasar.

CIkin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis da dare, Kwankwaso ya siffanta matakin na Tinubu a matsayin “mai haɗari ga dimokuɗiyya”.

InShot 20250309 102403344
Talla

A ranar talata ne Tinubu ya sanya dokar da ta dakatar da Gwamna Fubara, da majalisar dokokin jihar tare da maye gurbin gwamnan da kantoman riƙo saboda abin da ya kira “rashin doka da oda” sakamakon rikicin siyasa tsakanin Fubara da tsohon Gwamna Nyesom Wike.

Cin zarafi: Gwamnatin Kano za ta sanya kafar wando da sojojin baka – Kwamared Waiya

“Ina ganin rikicin siyasar da ake ciki a Rivers bai isa ya sa a ayyana sashe na 305(1) na kundin tsarin mulki ba,” in ji shi.

“Abin da ya fi damu na ma shi ne yadda majalisun dokokin ƙasa su ka amince da buƙatar shugaban ƙasa. Na yi fatan ba za su yarda da wannan abu da ya karya doka ba…Wannan mataki nasu zai kawo wa dimokuraɗiyyarmu cikas.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...