Ba a taba samun dan shugaban kasa mai son mutane kamar Seyi Tinubu ba – Adamu Karkasara

Date:

Daga Abubakar Yakubu

 

Hadimin mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Hon. Adamu Abdullahi Karkasara ya ce suna goyon bayan ziyara da rabon Abinchin da dan shugaban kasa Seyi Tinubu ke yi a arewacin Nigeria.

” Mun yi Shugabannin kasa da yawa har da Buhari da yake namu kuma makwabcinmu, amma dansa Yusuf ba ma ya yarda ya ga mutane, amma shi Seyi Tinubu ya yarda babansa yana shugabantarmu kuma ya shigo cikinmu har yana raba mana abinchi, wannan abun da yake yi ai ya fi ya’yan Shugabannin baya sau dubu”.

Adamu Abdullahi Karkasara ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa ta musamman da ya yi da jaridar Kadaura24 ranar Juma’a.

InShot 20250309 102403344
Talla

Ya ce tabbas abun da Seyi Tinubu ya yi yan Arewa ba wani dan shugaban kasa da aka taba yi a Nigeria daga kudu har Arewan da ya yarda yan Arewa mutane ne har ya shiga cikinsu.

“Na ku sun sami dama ba su yi ba, an samu wani ya zo yana shiga cikin mutane yana taimaka musu kuma kun fito kuna sukarsa, muna so masu sukarsa su sani muna goyon bayansa da shi da mahaifinsa Tinubu saboda sun yi mana abubuwan alkhairi a arewacin Nigeria”. Karkasara

Adamu Abdullahi Karkasara wanda na hannun daman Sanata Barau Jibrin ne ya kuma kalubalanci dan gwamnan Bauchi da yake cewa matasa jiharsu aiki suke bb bukata ba aminci ba, da ya fito ya fada mana Matasa nawa ya samawa aikin yi kuma matasa nawa ya inganta rayuwarsu?.

Cin zarafi: Gwamnatin Kano za ta sanya kafar wando da sojojin baka – Kwamared Waiya

” Daga lokacin da Seyi Tinubu ya fara shigowa cikin mutanen Arewa, yan Arewa da yawa sun yi kudi, kuma da kuke cewa yana raba abinchi ku fada mana mutanen Arewan ba sa bukatar abinchin ne? Kawai kun kasa taimakawa mutane shi kuma ya zo yana taimakawa mutane kuma kuna jin haushi”.

” Babbar sa’ar da Seyi Tinubu ya yi shi ne yadda mutane kirki irinsu Nasiru Ja’oji suka kewaye shi, to abun kirkin da yake yi ne wadancan mutanen da suka sami dama su ka kasa taimakon kowa su ke ki”. A cewar Karkasara

Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta dan shugaban kasa Seyi Tinubu a azumin nan ya zagaya wasu daga cikin Jihohin arewacin Nigeria, inda ya ke raba abinchi tare da yin bude baki da wasu daga cikin matasan Jihohin da ya je.

Sai dai wasu daga cikin yan Arewan na kalubalantar abun da Seyi Tinubu ke yi inda suke danganta shi da Siyasa, sai dai karkasara ya ce ko da saboda Siyasa yake abun da yake yi ya chanchanci a yaba masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...