Al’ummar garin Gwagwarwa sun jajantawa Matawallen Gwagwarwa bisa Iftila’in Gobarar Kwalema

Date:

Daga Khadija Sulaiman

Kungiyar Mutaimaki juna ta garin Gwagwarwa dake karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano ta mika Sakon ta na jaje ga Matawallen Gwagwarwa Barr. Ibrahim Isa Aliyu bisa Iftila’in Gobarar da ta saru a kamfaninsa dake Dakata.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar Abubakar Shehu Gwagwarwa ya aikowa Kadaura24.

InShot 20250309 102403344
Talla

” Mun damu sosai bisa wannan iftila’in da ya faru da dan uwanmu, Barr. Ibrahim Isa Aliyu wanda yake amfani da dukiyarsa wajen taimakawa al’ummar garin Gwagwarwa da Karamar hukumar Nasarawa baki daya”.

Sanarwar ta ce ” A madadin dukkanin al’ummar garin Gwagwarwa Muna mika sonmu na jaje ga Matawallen Gwagwarwa Barr Ibrahim Isa, muna addu’ar Allah ya bashi juriyar wannan babbar asara da aka yi, kuma muna Addu’ar Allah ya mayar masa da alkhairi”.

Gobarar Kwalema: Atiku Abubakar ya jajantawa Matawallen Gwagwarwa

Abubakar Shehu ya ce suna fatan gwamnatin jihar Kano za ta duba wannan asara da Matawallen Gwagwarwa ya yi domin duba yadda za a taimaka masa , saboda yawan al’ummar da suke cin abinci a kamfanin.

Daga karshe muna addu’ar Allah ya kare afkuwar hakan a nan gaba, kuma ya mayar masa da mafi alkhairin abun da ya rasa Ameen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...