Majalisar wakilan Nigeria ta Amince da dokar ta baci da shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya a jihar Rivers.
Yayin zamansu na ranar Alhamis, ƴan majalisar wakilan sun amince da gagarumin rinjaye ƙudirin shugaban ƙasar na ayyana dokar ta ɓaci a jihar Rivers.

Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito a ranar Talata ne Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar inda ya dakatar da gwamnan jihar da sauran zaɓaɓɓun shugabanni.