Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da nada wasu mukamai da karin girma a wani yunkuri na karfafa harkokin mulki da inganta ayyuka a gwamnatinsa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24.
Wadanda aka nada ko kuma aka karawa mukamai daban-daban sune kamar haka.

1- An nada Architect Hauwa Hassan Tudun a matsayin Manajan Darakta ta Hukumar Tsara Burane ta Kano (KNUPDA)
2- An nada Mustapha Muhammad a matsayin babban sakataren yada labarai na gwamna kuma mataimakin kakakin mai magana da yawun gwamnatin Kano Sunusi Bature D/Tofa
3- An nada Auwal Lawan Aramposu a matsayin mataimakin Manajan Darakta na Hukumar KAROTA.
4- An nada Dr. Tukur Dayyabu Minjibir a matsayin mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin noma.
Baya ga wadannan muhimman mukamai, Gwamna Yusuf ya amince da karin girma ga wasu manyan jami’ai guda biyu.
Gwamnan Kano ya Bayyana Matsayarsa Game da Hawan Sallah Karama a Jihar
1- Zulaihat Yusuf Aji ta samu mukamin mataimakiyar Manajan Darakta ta gidan radiyon jihar Kano.
2- Injiniya Abduljabbar Nanono ya zama mataimakin Manajan Darakta na KHEDCO.
A yayin da yake taya sabbin wadanda ya nada Murna, gwamnan Kano ya ba su tabbacin goyon bayansa, sannan ya bukace su da su yi aiki tukuru a kan ayyukansu domin bayar da ta su gudummawar don ci gaban jihar Kano