Ba za mu lamunci cin zarafi ko tozarta wasu da sunan Tashe ba – Hukumar Hisbah

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Hukumar Hisba ya jihar kano ta ce zata saka wando kafa daya da masu yin amfani da tashe wajen cin zarafin mutane

Haka kuma Hukumar ta Gargadi Iyaye da cewa su Jawa Yayansu kunne akan Yadda suke yin amfani da wanann dama wajen tayar da zaune tsaye da rigimar daba da satar kayan mutane da sunan tashe.

Hakan na kunshe ne wata sanarwa da Mataimakin Kwamandan Hukumar ta hisba na jihar kano mujahid Aminudden ya fitar aka rabawa Manema Labarai.

InShot 20250309 102403344
Talla

Ya ce, hukumar ta shirya tsaf domin daukar matakin da ya dace ga wadanda su ke kokarin mayar da tashe hanyar cin mutuncin wadanda basu da aure.

Mujahid aminudeen ya ce aure nufi ne na allah dan haka addini ya hana cin zarafin wani saboda baiyi aure ba, ta hanyar zuwa inda yake ana kada masa gwauro.

Da dumi-dumi: El-Rufa’i ya fice daga jam’iyyar APC

Mun shirya tsaf domin sanya idanu akan masu wanann dabi’a ta cin zarafin mutane da sunan tashe kuma zamu gurfanar da su gaban kotu acewar Mujahid Aminudden.

Idan za a iya tunawa a bisa al’adar malam Bahaushe daga ranar 10 ga watan azumi ake fara gudanar da al’adar tashe a yankin arewacin kasar nan, wanda kuma yanzu wanann al’ada take zama wata hanyar tayar da rikici musamman na fadan daba a wasu wurare.

Ko a Juma’ar makon da muka yi bankwana da shi, sai da lamaman masallatan juma’a suka yi ta kiraye-kirayen hukumomi a Kano su dauki matakin haramta tashen saboda abun da yake haifar na tashin hankalin al’ummar Musulmi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: El-Rufa’i ya fice daga jam’iyyar APC

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya tabbatar da...

2027: Atiku Abubakar ya bayyana matsayarsa game da kasancewarsa a PDP

  Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya musanta rahotannin...

Cikakken Bayani Kan Yan Bindigar da Yansanda Su Ka Kama a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar yansanda ta kasa reshen jihar...

Gidauniyar Sheikh Dr. Muhajihid Aminudden ta rabawa magidanta 600 kayan abinchi a Kano

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Gidauniyar Dr. Muhajihid Aminudden ta rabawa...