Gidauniyar Sheikh Dr. Muhajihid Aminudden ta rabawa magidanta 600 kayan abinchi a Kano

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Gidauniyar Dr. Muhajihid Aminudden ta rabawa magidanta a jihar Kano kayan abinchi domin saukaka musu a wannan azumin.

Da yake yiwa Kadaura24 karin haske Shugaban gidauniyar Dr. Muhajihid Aminudden ya ce sun raba kayan ne don saukakawa al’umma , musamman a wannan lokaci na watan azumin watan Ramadana.

InShot 20250115 195118875
Talla

” Muna mika godiyar mu da jagoran Kwankwasiyya Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa yadda suke taimakawa al’umma musamman a wannan lokaci”.

Dr. Muhajihid Aminudden wanda shi ne mataimakin kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano, ya ce masu hannu da shuni ne suka baiwa gidauniyar tallafin kayan abinchin domin ta rabawa mabukata.

” Muna bika godiya ga duk wadanda suka bayar da tallafin don a rabawa bayin Allah a wannan lokaci da Allah ya ke son bayinsa su rika yin aiyukan alkhairi, muna addu’ar Allah ya saka musu da Alkhairi”.

Gwamna Abba Gida-gida Ya Kaddamar Da Gyaran Hanyoyi 17 A Babban Birnin Kano

Ya kuma yi kira ga sauran mawadata da su rika tallafawa al’umma, musamman a wannan lokaci na azumin Ramadana, watan da aka rawaito cewa duk yawan kyatar manzon Allah Sallallahu alaihi wasallam idan azumin Ramadana ya zo ninninka kyautar yake yi saboda falalar watan na Ramadan.

Kayan da aka raba sun hadar da Shinkafa Masara, Taliya da makaroni da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

2027: Atiku Abubakar ya bayyana matsayarsa game da kasancewarsa a PDP

  Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya musanta rahotannin...

Cikakken Bayani Kan Yan Bindigar da Yansanda Su Ka Kama a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar yansanda ta kasa reshen jihar...

Gwamna Abba Gida-gida Ya Kaddamar Da Gyaran Hanyoyi 17 A Babban Birnin Kano

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da...

Dan uwan gwamnan Kano ya bar NNPP Kwankwasiyya

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...