Daga Rahama Umar Kwaru
Rundunar yansanda ta kasa reshen jihar Kano ta ce ta kama yan bindiga 4 uku da su ka shigo jihar Kano daga jihar katsina domin sayan bindigogi kirar AK-47.
Jami’in hulda da jama’a na Rundunar yansanda ta Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan yayin taron manema labarai a Kano.
SP Kiyawa ya ce sun kama mutanen ne a kan titin bypass kusa da gidan man Chula, inda ya ce dama sun sami labarin cewa mutanen za su shigo jihar Kano domin sayan bindigogi hakan yasa suka bibiyi lamarin har Allah yasa suka kama yan bindiga 3 da Wanda zai kai su su sayi bindigar mutum 1.

” Daga cikin wadanda aka muka kaman akwa Shukurana Salihu mai shekaru 25, sai Rabi’u Dahiru dan shekaru 35, sai Ya’u Idris mai shekaru 30 kuma dukkaninsu yan jihar katsina ne, sai dan jihar Kano da aka hada baki da shi Mukhtar Sani dan unguwar Hotoro, kuma dukkaninsu yanzu haka suna nan helkwatar yansanda ta Kano dake Bompai”. Inji SP Abdullahi Kiyawa
Ya ce lokacin da aka kama su an same su da bindigogi guda 3 da harsasai masu yawa da boris da wukake da kuma kudi Naira Miliyan 1 da dubu 28 da dari 8.
Gidauniyar Sheikh Dr. Muhajihid Aminudden ta rabawa magidanta 600 kayan abinchi a Kano
Kiyawa ya ce tuni sun fara binke kuma da zarar sun kammala za a mika su kotu don girbar abun da suka shuka.
Ya kuma yabawa al’ummar jihar Kano bisa hadin kan da suke ba su, sannan ya bukaci su cigaba da basu bayanan sirri domin dakile aiyukan taa’addanci a fadin jihar Kano.