Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya musanta rahotannin da ke cewa ya bar jam’iyyar PDP.
Dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023 ya sake jaddada goyon bayansa ga hadakar jam’iyyun siyasa don kayar da jam’iyyar APC a 2027.

Daily Trust ta rawaito cewa, a baya-bayan nan, rahotanni daban-daban sun nuna cewa Atiku yana tunanin barin PDP don shirin takarar shugaban kasa a 2027.
Rahotannin sun ce yana shirin komawa jam’iyyar SDP.
Amma a cikin wata sanarwa da ofishin yada labaransa ya fitar a ranar Asabar, an bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasar na nan a matsayin cikakken mamba na PDP.
Gidauniyar Sheikh Dr. Muhajihid Aminudden ta rabawa magidanta 600 kayan abinchi a Kano
Yayin da yake karyata rahotannin a matsayin “karya tsagwaronta”, ofishin yada labaran ya bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da su.
Ofishin yada labaran ya jaddada cewa Abubakar ya dade yana kira da a hada kawancen jam’iyyun adawa a Najeriya domin cire APC daga mulki a 2027.