Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa ya karbi guda cikin yan uwan gwamnan Kano Mahbub Nuhu Wali da sauran magoya bayan jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sanatan ya wallafa a sashin shafinsa na Facebook.
Ya karbi makusantan gwamnan daga jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya zuwa jam’iyyar APC.

” A yau na karbi sakataren kungiyar Malamai ta Kwankwasiyya Malam Yahaya Abdulkadir Aliyu da wasu daga cikin Shugabanni kungiyar su 23 zuwa jam’iyyar APC”. Inji Sanata Barau
Daga ofishina suka biyo ni zuwa A-Class Event Centre, inda muka karbi wasu kungiyoyi da suka goyi bayan Atiku Abubakar a zaben 2023 daga jihohin Arewa 19.
Ya ce bayan taron ne shugaban jam’iyyarAPC na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya tarbe su a hukumance cikin jam’iyyar mu.
Yanzu-yanzu: Yansanda sun kama yan bindiga a Kano
Shugabannin jam’iyyar NNPP guda biyu daga karamar hukumar Gwale ta jihar Kano, Mahmoud Salisu Gwale da Farouk Ahmed Gwale, suma sun dawo jam’iyyar ta su .
A wajen taron karbar ta su zuwa jam’iyyar APC, Barau ya jaddada kudirinsa na inganta rayuwar al’ummar mazabar Kano ta Arewa, Jihar Kano, Arewa, da kasa baki daya.
“A matsayina na mataimakin shugaban majalisar dattawa, ina so in jaddada cewa ni Sanata ne ga kowa da kowa. Ba tare da la’akari da siyasarka ba – ko kai dan PDP ne, ko LP, ko Kwankwasiyya, ko ma dan jam’iyyar APGA – Kofofina a bude suke ga kowa. Idan kuna son shiga jam’iyyarmu ta APC, jam’iyyar jama’a, muna yi muku maraba”.