Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya Godswill Akpabio ya musanta zargin cin zarafi ta hanyar lalata da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi a kansa.
Ya musanta zargin ne a ranar Laraba bayan majalisar ta koma aiki daga gajeren hutun da ta tafi.

Sanata Akpabio ya nuna rashin jin daɗinsa game da abubuwan da ke yawo a shafukan sada zumunta kan zargin da ake masa inda ya yi watsi da shi baki ɗaya.
“Ban taɓa cin zarafin wata mace ba. Na samu tarbiyya daga mahaifiyata, kuma ina girmama mata. An taɓa ba ni lambar yabo ta gwamnan da ya fi kyautata wa mata a Nijeriya,” kamar yadda Sanata Akpabio ya bayyana.
An sake samu tsaiko a shari’ar neman a hana kananan hukumomin Kano kudadensu
Bayan nan ne sai Sanata Natasha ta miƙe tsaye ta gabatar da korafi a kansa a hukumance a gaban majalisar bisa zarge-zargen da take masa.
A yayin da take gabatar da ƙorafin, ta zargi Akpabio da cin zarafi ta hanyar lalata da amfani da ƙarfin iko ba bisa ƙa’ida ba da kuma tauye mata haƙƙinta na gudanar da ayyukan majalisa.
Bayan ta gabatar da ƙorafin sai shugaban majalisar ya buƙaci kwamitin majalisar kan kula da ɗa’ar ‘yan majalisa da karɓar ƙorafe-ƙorafe ta yi aiki kan zargin.
Wannan na zuwa ne bayan an shafe kwanaki ana ce-ce-ku-ce kan wannan lamarin bayan Sanata Natasha ta yi wannan zargin a wani gidan talabijin a Nijeriya