Daga Rahama Umar Kwaru
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi rashin mai ba shi shawara na musamman kan kabilu, Alhaji Abdussalam Abiola Abdullateef.

‘yan uwan mamacin ne suka tabbatar wa majiyar kadaura24 ta SolaceBase cewa Abdussalam ya rasu ne a ranar Asabar bayan gajeriyar rashin lafiya kuma an yi jana’izarsa da yammacin yau a makabartar Hajji Camp.
Da dumi-dumi: An kama wani shugaban karamar hukuma a Kano
SolaceBase ta ruwaito cewa mashawarcin na musamman dan asalin jihar Osun ne, ya kammala karatunsa ne a fannin lissafi a Jami’ar Bayero Kano, kuma kwanan nan ya yi ritaya daga aiki a Asibitin Orthopedic ta kasa da ke Dala a Kano.
Idan za a iya tunawa Abdussalam Abdullateef ya taba rike irin wannan mukamin daga 2011 zuwa 2015 a lokacin mulkin Engr. Rabiu Musa Kwankwaso