Ramadan: Hukumar Hisba ta Kama Gandaye a Kano

Date:

 

Jami’an Hukumar Hisba a jihar Kano sun kama wasu matasa gandaye da ake zargi da kin yin azumi a ranar farko ta watan Ramadan.

Mataimakin babban kwamandan hukumar, Dakta Mujahideen Abubakar ne ya tabbatar da kamen ga manema labarai a jihar.

Ya kara da cewa an kama matasan ne yayin sintiri da jami’an hukumar ke yi a sassa daban-daban na birnin Kano.

InShot 20250115 195118875
Talla

Haka kuma, hukumar ta cafke kimanin mutane 60 da ke da askin banza, wanda ya sabawa dokokin shari’a da al’adun gari.

Jimami: Hadimin Gwamnan Kano ya Rasu

Bugu da kari, Hisba ta kama wasu direbobin baburan adaidaita sahu (keke napep) da ake zargi da cakuda maza da mata a baburansu, lamarin da hukumar tace ba za ta lamunta da shi ba.

Daily Nigerian ta rawaito Hukumar ta Hisba ta bayyana cewa za ta ci gaba da gudanar da sintiri don tabbatar da bin dokokin shari’a a cikin watan Ramadan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...