Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya tabbatar da cewa an ga watan Ramadana a Nigeria
“Mun sami labarin ganin watan Ramadana a Wannan rana ta Juma’a, kuma muna tantance mun kuma amince da Batun ganin watan, don haka gobe ne 1 ga watan Ramadana”.

Kadaura24 ta rawaito Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a fadarsa dake Sokoto.
Yanzu-Yanzu: An ga Watan Ramadan a Ƙasar Saudiyya
Bisa Wannan bayani na Sarkin musulmi ta tabbaa gobe asabar ne 1 ga watan Ramadan na Shekarar 1446 Bayan Hijr.
Dama dai yau Juma’a ne 29 ga Watan sha’aban Kuma ita ranar da mai alfarma sarkin musulmi ya bada Umarnin a fara duban jinjirin watan duban wata a Nigeria.