Burinmu shi ne Barau FC ta sami gurbin shiga gasar zakarun Nahiyar Africa – DSP Barau

Date:

Daga Ahmad Hamisu Gwale

 

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria, Dr. Barau Jibrin, ya bayyana matukar sha’awarsa na ganin kungiyar kwallon kafa ta Barau ta sami gurbin shiga gasar zakaru ta Nahiyar Afrika (CAF) a bana.

Sanata Barau wanda shi ne shugaban kungiyar ya bayyana haka yayin da yake karbar bakuncin shugaban kungiyar ta Baraub FC Ambasada Ibrahim Shitu Chanji a Kano ranar Litinin.

Ya kuma yabawa da yadda aka yi wasan karshe na gasar cin kofin shugaban kasa a jihar Kano da aka yi tsakanin Kano Pillars da Barau FC a ranar Lahadi inda Kano Pillars ta yi nasara da 3-2 .

InShot 20250115 195118875
Talla

“Ina so in yaba da yadda aka buga wasan karshe tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da kungiyar Barau FC a gasar cin kofin kwallon kafa na shugaban kasa a jihar Kano, wannan babban nasara ce a samu kungiyoyi biyu masu karfi kuma su fafata da juna a wannan matakin a Kano,” in ji Sanata Barau.

Ya kara da cewa “Babban abin da na fi mayar da hankalina da kuma damuwa shi ne na tallafa wa kungiyar kwallon kafa ta Barau FC ta kowace hanya ta yadda za ta wakilci Najeriya a gasar cin kofin Afrika, burinmu shi ne ganin kulob din ya shiga gasar cin kofin zakarun Nahiyar Africa a bana.”

Gaskiyar Lamari Game da Rikicin Darikar Kadiriyya

A matsayin ta na biyu a gasar cin kofin shugaban kasa na jihar Kano, kungiyar Barau za ta wakilci jihar a gasar cin kofin kwallon kafa na shugaban kasa ta Najeriya a bana.

IMG 20250225 WA0013

A ranar Laraba 12 ga watan Maris ne za a fitar da jadawalin wasannin cin kofin kwallon kafa na shugaban kasa na shekarar 2025, inda za a fara zagaye na 64 a ranar 19 ga Maris.

Wanda ya lashe gasar PFC ta 2025 kai tsaye shi zai sami tikitin shiga gasar cin kofin zakarun Nahiyar Africa a shekara mai zuwa, kuma Barau FC na fatan samun damar wakiltar Najeriya a gasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...