Gwamnatin Kano ta Sanya Ranar Rufe Makarantun Firamare da Sakandire

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Gwamnatin jihar Kano ta amince da ranar juma’a 28 ga watan fabarairu, 2025, a matsayin ranar hutun Zango karatu na biyu ga makarantun firamare da sakandire dake jihar baki daya.

A wata sanarwa da daraktan wayar da kan al’umma na ma’aikatar ilimi ta jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru ya aikewa manema labarai , ya ce hutun ya shafi makarantu masu zaman kansu da na gwamnati .

InShot 20250115 195118875
Talla

Sanarwar ta ce daliban makarantun firamare da sakandire na kwana za su koma Makarantunsu a ranar lahadi 06 ga watan Afirilu,2025, su kuma na makarantun jeka ka dawo za su koma Makarantar ranar litinin 07 ga watan Afirilu, 2025.

Gwamnan Kano ya lashe lambar yabo ta gwamna mafi ƙwazo a Afirka

Kwamishinan ilimi na jihar Kano Dr. Ali Haruna Makoda ya bukaci iyayen yaran da su tabbatar da cewa ya’yansu sun koma Makarantar a ranakun da aka sanya.

Sanarwar ta gargadi masu makarantu masu zaman kasansu da su tabbatar da bin ka’idar da aka gindaya ko kuma su fuskanci hukunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...