Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa
A karshen makon da mu ka yi bankwana da shi ne rahotanni su ka yi ta fita cewa shugaban darikar Kadiriyya na Duniya Sayyid Shehu Afifudden aljilani, ya nada Malam Ibrahim Isa Makwarari a matsayin sabon khalifan darikar Kadiriyya na Nigeria.
Babu shakka wadancan bayanai sun yamutsa hazo sosai, wanda hakan ya al’umma musamman mabiya darikar Kadiriyya suka shiga rudani kan wa za su bi a matsayin jagoransu tsakanin Khalifa Sheikh Karibulla Muhd Nasiru Kabara da kuma Malam Ibrahim Isa Makwarari.
Duka dai a wancan satin Malam Ibrahim Isa Makwarari ya gudanar da taron manema labarai, inda ya bayyana kansa a matsayin sabon khalifan darikar Kadiriyya na Nigeria.
A yayin taron Malam Ibrahim Isa ya ce za su gyara duk wasu abubuwa wadanda mabiya darikar ba sa jin dadinsu, har ma yayi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta gaggauta sakin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara wanda yake gidan yari sakamakon laifin yin kalaman batanci da aka same shi da shi.
“Darikar Kadiriyya ta yanzu ba zata bari a ci zarafin danta ba, don haka muna kira ga gwamnatin jihar Kano karshin gwamnan Alhaji Abba Kabir Yusuf da ya tabbatar an yi abun da ya dace don sakin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara”. Inji Malam Ibrahim Isa
Sai dai tun da ake wannan dambarwa Sheikh Karibulla Nasiru Kabara bai ce komai ba akan wanne lamari.

Wannan ta sa jaridar Kadaura24 ta bibiyi lamarin don gano waye hakikanin khalifan darikar Kadiriyya da kuma gano masu kokarin haifar da rudani da raba kan mabiya darikar Kadiriyya a Nigeria.
A wani sahihin bidiyo da jaridar Kadaura24 ta gani, mun ji yadda Amb. Dr. Shehu Abdulkadir wanda ake yi masa lakabi da Sarkin Darikar Kadiriyya na Africa Wanda shi ne ya kawo Khalifan darikar Kadiriyya na Duniya Sayyid Shehu Afifidden aljilani jihar Kano.
Yanzu-yanzu: NNPP ta dakatar da Sanata Kawu Sumaila da wasu yan Majalisar wakilai a Kano
Ya ce ” A gaskiya ni na kawo maulana sayyid Afifudden aljilani jihar Kano bayan an gama Maulidi, bayan ya zo mun je ya aza harsashin ginin Makarantar da masallacin da nake son ginawa, daga nan mu ka tafi da shi ya ziyarci kabarin Amirul jaishi ( Sheikh Nasiru Kabara), ya kuma je ya sa albarka a masallacin malam Askiya, daga nan sai muka zo gidana inda na shirya masa gagarumar hallara”.
“Bayan an gama hallarar ne shi Malam Ibrahim Isa Makwarari, ya zo ya same ni da rawaninsa a aljihunsa, ya ce na fadawa Shehi yana so a saka masa albarka na rabidatul Muhammadiyya, kuma haka Shehi ya sa masa albarka a matsayinsa na shugaban rabidatul Muhammadiyya , amma ba nadin khalifan darikar Kadiriyya aka yi masa ba”. Inji Amb. Shehu Abdulkadir jimoh
Ya ce a gidansa akai duk abun da akai kuma a gabansa ba wai a wani waje akai ba, don haka ya sake tabbatar da cewa a Shehu Afifudden aljilani bai nada wani a matsayin Khalifan darikar Kadiriyya na Nigeria ba.