Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibril ya bayar da gudummawar motoci 61 da babura 1,136 ga shugabannin jam’iyyar APC a jihar Kano.
Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa ya ruwaito cewa an yi rabon ne da nufin karfafa ‘gwiwar ya’yan jam’iyyar APC da kuma saukaka gangamin goyon bayan jam’iyyar tun daga tushe a jihar.

Jibril ya ce za a raba baburan ga shugabannin jam’iyyar na mazabu, yayin da motocin kuma za a raba su ga shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomi da na shiyya-shiyya.
Sabon Rikici Ya Kunno Kai Cikin Jam’iyyar APC a Kano
Ya kuma bayyana shirin baiwa dalibai da suka kammala jami’a rancen kudi Naira miliyan 5 domin fara kananan sana’o’i.