Manyan Kusoshin NNPP da ‘yan majalisu na shirin dawowa APC – Ganduje

Date:

 

Shugaban jam’iyyar All APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa jam’iyyar ta shirya tarbar sauya sheƙa daga wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar NNPP, wacce ya bayyana a matsayin “jam’iyyar da ke dab da mutuwa.”

Ganduje ya bayyana hakan jiya yayin rabon motocci 63 da babura 1,137 ga shugabannin APC na kananan hukumomi da mazabu a faɗin Jihar Kano. Wannan shiri na ƙarfafa jam’iyya da tallafa wa mambobinta ya samu ɗaukar nauyi daga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa, Sanata Barau Jibrin.

Sabon Rikici Ya Kunno Kai Cikin Jam’iyyar APC a Kano

“Wannan shirin tallafa wa al’umma ba wai ga mambobin APC kaɗai ba ne, har ma da al’ummar Kano baki ɗaya. Zai taimaka wajen inganta rayuwar mutane da samar da ayyukan yi,” in ji Ganduje.

Kowane shugaban APC na ƙaramar hukuma zai karɓi mota, yayin da shugabannin mazabu a cikin mazabu 484 na jihar za su samu babura. Saboda wasu dalilai na dabaru, an raba takardun mallakar kayan a wajen taron, inda aka umurci masu cin gajiyar su je su karɓi kayan daga baya.

InShot 20250115 195118875
Talla

Ganduje ya jinjinawa mambobin jam’iyyar saboda ƙwazon su da biyayya, yana mai nuna tabbacin cewa wasu manyan jiga-jigai, ’yan majalisa da sanata-senata daga NNPP za su sauya sheƙa zuwa APC nan ba da jimawa ba.

“Dubban mutane na shirin shigowa cikin wannan babbar jam’iyya. Nan bada daɗewa ba za mu tarbi wasu fitattun jiga-jigai daga waccan jam’iyya da ke dab da durƙushewa,” Ganduje ya bayyana.

Ya kuma yaba da jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce gyare-gyaren tattalin arziki da gwamnatinsa ke aiwatarwa sun rage farashin mai, farashin abinci, tare da ƙarfafa darajar Naira.

A nasa jawabin, Sanata Barau Jibrin ya bayyana shirin a matsayin mataki na farko na wani babban shiri na tallafawa jama’a daban-daban.

Inganta ilimi: Jaridar New Telegraph ta Karrama Gwamnan Kano

“Wannan babban shiri ne da muka fara da shugabannin jam’iyya. Ta hanyar basu motocci da babura, muna inganta rayuwarsu da samar da ayyukan yi,” in ji shi.

 

Jibrin ya ƙara da cewa waɗanda suka ci gajiyar tallafin za su yi amfani da motocin ba kawai don bukatunsu na yau da kullum ba, har ma don samar da ayyukan yi. Ya kuma tabbatar da cewa matakai na gaba za su mayar da hankali ga matasa, ’yan kasuwa da manoma.

“Ba za mu bar kowa a baya ba. Wannan shi ne farkon tafiya,” in ji shi, yana mai ƙara da alƙawarin ci gaba da tallafawa Kano da Najeriya baki ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...