Daga Kamal Yakubu Ali
Sabon shugaban hukumar zakka da Hubusi ta jihar kano sheikh Barrister Habibu Muhammad Dan almajir ya bukaci mawadatan da ke cikin al’umma da hukomomi da su ba su hadin kan da ya kamata domin gudanar da ayyukanta kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Barrister Dan almajir ya ce zakka rukuni ce daga cikin rukunun addinin musulunci, domin bayan tauhidi da sallah sai kuma zakka, a don haka yake bukatar mutane su basu cikakken hadin kai domin gudanar da aikin kamar yadda gwamna Alhaji Abba kabir ya ba su amanar gudanar da aikinsu ba tare da nuna bambanci ba .

Yace kofar hukamar a bude take ga duk wanda ya ke bukatar zai rabawa al’ummarsa zakka a duk inda yake da ya gaiyato jami’an hukumar da su zo su raba masa ko kuma su shaida yadda rabon yake gudana ko ya Raba gida biyu ya baiwa hukumar kaso daya su ma su je su baiwa mutane domin su yi masa shaida a duniya da lahira.
Sheikh Dan àlmajiri yace hukumar zakka an samar da ita ne domin karbar zakka daga hannun mawadata da suke cikin al’umma da kuma rabata ga mabukata, wanda hakan ya ke tallafawa mubuka wajan rage Talauci da fatara da kuma sanya kauna a tsakanin al’umma .
Yadda Gwamnan Kano ke shirin zamanantar da sana’ar fawa – Hon. Sani Rabi’u Rio
Ya ce “Za mu yi iya kokarinmu duk abin da aka kawo mana hukumarmu a matsayin zakka zamu Rabata ga mabukata ba tare da mun Tauye komai ba a ko ina a fadin jihar nan.
Ya ce a yanzu nisabin zakka ta kudi ya kai kimanin Naira Miliyan goma sha daya da dubu dari bakwai da chasain da shida da dari biyu da Arbain 11,796240. Sai kuma zakka kayan Noma da dabbobo da sauransu.
Sheikh Dan almajir ya ce hukumar za ta rika fitar da bayanan a game da zakka domin kara tunatar da alumma ta kafafan yada labarai