Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ya alkawarin kammala dukkanin aiyukan da tsohuwar gwamnatin Ganduje ta yi watsi da su a jami’ar Kimiya ta Aliko Dangote dake karamar hukumar Wudil.
Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci jami’ar domin ganin halin da jami’ar take ciki.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24 ya ya ce gwamnan ya zagaya jami’ar bisa rakiyar shugaban jami’ar Musa Tukur Yakasai.

Ya yiwa dalibai da malaman jami’ar alkawarin kammala dukkanin aiyukan da ba a kammala su, inda ya ce jami’ar ta na da matukar amfani ga al’ummar jihar Kano da ma kasa baki daya.
” Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya samar da Wannan jami’a tun a Zangon mulkinsa na farko, kuma jami’ar ta yaye inginiyoyi daga fannoni daban-daban, don haka dole mu sake zage damtse wajen inganta ta”.
Kwanaki 100: Shugaban karamar hukumar Wudil ya kaddamar da wasu aiyukan raya kasa
Sanarwar ta ce a kokarinsa na bunkasa jami’ar ta Wudil, gwamna Abba Kabir Yusuf ya kara baiwa jami’ar fili kadada 100, wanda jami’ar za ta yi amfani da shi wajen samar da sabuwar tsangayar koyar da harkokin inginiya da kuma gini majalisar kolin jami’ar.
Ya kuma kara da cewa gwamnatinsa tana baiwa Ilimi fifiko ne saboda shi ne ginshikin rayuwar duk wata al’umma .
A jawabinsa shugaban jami’ar ta Aliko Dangote dake Wudil Farfesa Musa Tukur Yakasai ya roki gwamnan da ya gaggauta biyan diyyar masu filaye a kusa da jami’ar domin samun damar yin aikin akan lokaci.