Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Gwamnatin jihar Kano ta ce ta gamsu da sabbin tsare-tsaren Bankin ba da lamunin gidaje na gwamnatin tarayya, hakan ta sa ta mayar da ma’aikatan jihar cikin tsarin .
” A bayan gwamnatin jihar Kano ta fita daga tsarin ne saboda rashin tabbas na tsarin da kuma yadda ma’aikata ba sa sanin hakikanin kudin da ake yankar musu, hakan ta sa gwamnatin a wancan lokacin ta ga dacewar ta fitar da ma’aikatan jihar Kano da tsarin ba da lamunin gidaje na gwamnatin tarayya”.
Shugaban ma’aikatan jihar Kano Abdullahi Musa ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa ta musamman da ya yi da jaridar Kadaura24 a Kano.

Ya ce kafin mayar da ma’aikatan jihar Kano cikin tsarin a wannan karon sai da gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamiti karkashin shugaban ma’aikata domin gano matsalolin da kuma yadda za a magance su don ma’aikatan jihar Kano su cigaba da amfana daga tsarin.
” Bayan mun gano matsalolin, kwamitin ya tashi daga nan har Abuja muka zauna da shugabannin bankin kuma suka gaya mana cewa wadancan matsalolin duk sun kau saboda sabuwar fasahar zamani da ake amfani da ita domin sanar da ma’aikaci abun da aka yanke masa da kuma abun da ya tara”. Inji Shugaban ma’aikatan Kano.
Gwamnan Yusuf ya yi alkawarin kammala aiyukan da Ganduje ya yi watsi da su a jami’ar Wudil
Ya ce bayan sun gamsu da bayanan da suka dawo suka rubutawa gwamna rahoto na amincewa a koma tsarin, kuma gwamnan ya amince har aka tattauna batun a zaman majalisar zartarwa ta jihar in da aka Amince za a mayar da ma’aikatan jihar Kano cikin tsarin bankin ba da lamunin gidaje na gwamnatin tarayya.
Abdullahi Musa ya baiwa ma’aikatan jihar Kano tabbacin za su ji dadin tsarin saboda alfanun da yake da shi, inda ya ce da yawa za su sami gidaje kafin su kammala aiki da kuma samun rance na kudin gyara gidaje ga mai bukata.