Sanusi Bature da Abokansa Sun Tallafawa Wata Makarantar Islamiyya da Naira Miliyan 3 a Kano

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa shi da abokansa sun tallafawa wata Makarantar Islamiyya mai suna Hayatul Islam dake karamar hukumar Tofa da Naira Miliyan 3 .

Sanusi Bature da abokan nasa sun bada tallafin ne yayin bikin saukar karatun Alqur’ani mai girma Wanda aka gudanar yau asabar a garin Tofa.

Da yake jawabi a wajen bikin saukar karatun Alqur’anin , Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce sun bayar da tallafin kudin ne don inganta harkokin koyo da koyarwa a Makarantar.

InShot 20250115 195118875
Talla

” Babu shakka wadannan daliban sun yi kokarin sauke Alqur’anin mai girma, kuma suma Malamansu sun taimaka bisa yadda suka tsaya tsayin daka don ganin wadannan dalibai sun sami ilimin addini”. Inji Dawakin Tofa

Ya ce a matsayinsu na wadanda suka san muhimmancin Ilimin Alqur’anin, ya zama wajibi su tallafawa duk wani sha’ani da ya shafi Alqur’anin da addinin musulunci baki daya.

Matsalar tsaro: Gwamna Kano ya kafa Kwamitin karta-kwana

” Halin Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ne tallafawa duk abun da ya shafi ilimi saboda kishinsa da ilimi, shi yasa barewa ba zata taba yin gudu ba danta ya yi rarrafe”.

Wannan dai ba shi ba ne karon farko da Sanusi Bature Dawakin Tofa mai magana da yawun gwamnan Kano yake taimakawa makarantun Islamiyya don inganta harkokin Ilimin Alqur’anin da na addinin musulunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sabon Rikici Ya Kunno Kai Cikin Jam’iyyar APC a Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Karamin Ministan gidajen da raya burane...

Yadda Manoma a Nigeria ke cigaba da kokawa saboda karyewar farashin kayan abinchi

  Farashin kayan abinci kamar masara, gero da shinkafa na...

Inganta ilimi: Jaridar New Telegraph ta Karrama Gwamnan Kano

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Sanarwa ta musamman ga masu neman shiga aikin dansanda

Hukumar kula da aikin 'yan sanda na Kasa (POLICE SERVICE...