Gidauniyar Da’irar ma’aiki (S A W) ta rabawa marayu da masu bukata ta musamman suturu a Kano

Date:

Daga Abubakar Gwagwarwa

 

Shugabar Gidauniyar Da’irar ma’aiki Sallallahu alaihi wasallam Sayyada Hauwa Aminu Inuwa (yar aljanna) ta bayyana cewa gidauniyar ba zata gajiya ba wajen tallafawa marayu da masu bukata ta musamman don inganta rayuwarsu.

“Duk talaucinka idan ka duba baya za ka ga akwai wanda ka fi, hakan ta sa dan abun da Allah ya hore mana muke tallafawa al’umma daidai gwargwado, kuma ba za mu gajiya ba in Allah ya so”.

Sayyada Hauwa Aminu Inuwa ta bayyana hakan ne lokacin da ta jagoranci gidauniyar Da’irar ma’aiki S A W wajen tallafawa marayu da masu bukata ta musamman dake Garin Gwagwarwa a Kano.

InShot 20250115 195118875
Talla

” A wannan lokaci al’umma suna cikin mawuyacin hali, shi yasa muka ga akwai bukatar mu yi rabon suturu saboda talauci ya sa al’umma da dama suna yawo tsaraicinsu a waje, amma da dan rabon suturu da muka yi mun yi imani mun suturta wadanda suka samu, muna kuma fatan Allah ya karba mana”.

Ta ce da fari an samar da kungiyar Da’irar ma’aiki ne saboda koyar da harkokin yabon ma’aiki S A W, daga bisa ni kuma sai suka ga dacewar fadada aiyukan kungiyar zuwa tallafawa masu karamin karfi dake cikin al’umma.

Matsalar tsaro: Gwamna Kano ya kafa Kwamitin karta-kwana

Da take jawabin sakatariyar kungiyar ta Da’irar ma’aiki (S A W) ta ce akalla mutane 20 ne suka amfana da tallafin kayan, wadanda suka hadar da kayan maza da na mata.

” Babu shakka yau babbar rana ce a wajenmu saboda nasarar da muka samu na raba wadannan kaya, kuma muna kira ga masu hannu da shuni da su taimaka mana don mu cigaba da tallafawa masu karamin karfi dake cikin al’umma.

Wasu daga cikin wadanda suka amfana da tallafin kayan yawar, sun yabawa kungiyar ta Da’irar ma’aiki Sallallahu alaihi wasallam bisa yadda suka tallafa musu, sannan suka yiwa Shugabannin kungiyar fatan alkhairi.

Sun kuma yi kira ga masu hannu da shuni da su rika tallafawa masu karamin karfi don inganta rayuwarsu da rage musu radadin halin da suke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...