Kungiyar ma’aikatan hukumar kula da kananan hukumomin Nigeria ta yabawa Gwamnan Kano

Date:

Ƙungiyar ma’aikatan hukumar kula da kananan hukumomi ta Ƙasa, ta yaba wa gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa nada Alhaji Ibrahim Jibril Fagge, a matsayin Shugaban Hukumar Kula da aiyukan kananan hukumoni ta jihar Kano.

Wannan na kunshe cikin sakon taya murna, da Shugaban Kungiyyar na Kasa Barrister Muhammad Sani Bawa, ya aike wa Alhaji Ibrahim Jibril Fagge.

A sakon, ya jinjinawa gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa farfado da hukumar a jihar Kano, da kuma danka shugabancin hukumar ga Alhaji Ibrahim Jibril Fagge, wanda gogagge ne a aikin-gwamnati, kuma akwai kyakkyawan zaton zai yi abin da ya dace, don ciyar da jihar Kano gaba.

InShot 20250115 195118875
Talla

Sanarwar ta kara da cewa, wannan mataki da gwamnan ya dauka, na nuni da irin kokarin gwamnan na bujuro da kyawawan tsare-tsare da za su ciyar da jihar Kano gaba.

Batan Bindigu: Babban Sufeton Yansandan Nigeria ya Roki Majalisa

Shugaban kungiyar Barr. Muhammad Bawa ya yi fatan Alhaji Ibrahim Jibril Fagge zai yi aiki tukuru domin ciyar da jihar Kano gaba, sannan kuma ya fitar da kungiyar kunya.

Kungiyar ma’aikatan hukumar kula da kananan hukumomin ta Kasa dai tana da rassa a dukkanin Jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...