Sifeto Janar na ƴansanda Najeriya, Kayode Egbetokun ya rubuta wa majalisar dattawa wasiƙa yana roƙonta cewa binciken da za a ci gaba da yi dangane da ɓatan bindigogi 3,907 ya kasance a sirrance bisa dalilan tsaro.
Sai a wasiƙar, sifeto janar na ƴansandan ya yi watsi da rahoton 2019 da ofishin babban mai bincike da gwamnatin tarayya ya fitar wanda ya yi ikrarin ba a san inda dubban bindigogin ƴansanda suka shiga ba ya zuwa watan Janairun 2020 inda ya bayyana rahoton da cewa cike yake da kurakurai.

Wasiƙar wadda aka karanta ta a majalisar dattawa bayan amince wa da kasafin kuɗin ƙasar na 2025 a ranar Alhamis, na zuwa ne sa’a 48 bayan wani zaman saurare da kwamitin majalisar dattawa mai binciken kashe-kashen kuɗaɗen gwamnati inda rundunar ƴansandan ta yi ta nuƙu-nuƙu wajen kare kanta.
Ba wani maniyaci dan Nigeria da zai rasa Aikin Hajjin bana – Shugaban NAHCON
Sifeto Janar na ƴansandan, kayode Egbetokun wanda ya kasance a wurin sauraron bahasin ranar Talata kafin daga bisani ya nemi uzuri ya bar zaman, ya soki yadda ake neman titsiye rundunar ƴansandan ƙasar a bainar jama’a.
Ya ƙara da cewa bai dace a rinƙa tattuna irin waɗannan batutuwan a bainar jama’a ba.