Tinubu 2027: Kungiyar ACF ta bar jaki ta na bugun taiki – Auwal Ibrahim Sansani

Date:

Daga Nasiru Waziri

 

 

Shugaban kungiyar Tinubu Northern Youth Forum Auwal Ibrahim Sansani ya kalubalanci sukar da kungiyar tuntuba ta Arewa wato ACF ta yi game da kalaman shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje na cewa duk mai bukatar takarar shugaban kasa daga Arewa ya hakura har sai Tinubu ya kammala shekarunsa 8.

Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito kungiyar ACF ta yi Kungiyar tuntuba ta Arewa ACF ta bayyana cewa babu wanda zai iya tilastawa yankin sake zaben Tinubu a shekara ta 2027.

InShot 20250115 195118875
Talla

A wata sanarwar da Auwal Ibrahim Sansani ya aikowa Kadaura24, ya ce sun rasa me yasa kungiyar ACF din ta ke kin Shugaban kasa Bola Tinubu duk kuwa da kokarin da yake na dora Nigeria a turbar cigaba.

” Dama kungiyar ACF ta dade tana nuna cewa ba zata goyi bayan Tinubu a zaben shekara ta 2027 ba, saboda a baya tsahon dakataccen shugaban kungiyar Mamman Osuman ya fito karara ya bayyanawa duniya cewa a 2027 ba za su goyi bayan duk dantkarar da ba daga Arewa ya fito ba, wanda hakan tasa kungiyar ta ce ta dakatar da shi daga mukaminsa”. Inji Auwal Ibrahim Sansani

Kungiyar ACF ta yi wa Ganduje martani

Ya ce duk da kokarin da Tinubu ya ke na inganta tattalin arzikin Nigeria da dora kasar a turbar cigaba, amma sun fahimci tuni kungiyar ACF ta tsayar da matsayarta.

” Ya kamata ACF ta sani da yawa daga cikin yan Arewa za su barawa Tinubu baya, sabani da matakin da kungiyar ta dauka, wanda ba ya daga cikin manufofin da su ka sanya aka kafa kungiyar ta ACF”. Auwal Ibrahim Sansani

Jaruma Maryam Malika ta roƙi kotu da ta tabbatar da sakin da mijinta ya yi mata

Shugaban kungiyar Northern Youth Forum ya ce kamata ya yi kungiyar ACF ta marawa Tinubu baya domin ya sami nasarar da ya sanya a gaba wajen kawo aiyukan cigaba jihohin Arewacin Nigeria.

 

Ya ce Shugaban kasa Bola Tinubu shi ya kamata yan Arewa su sanya a gaba saboda manufofin ciyar da yankin gaba da yake da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...