Abdulmumin Jibrin Kofa ya gabatar da kudirin kafa jami’a a Kano da wasu 15

Date:

Daga Zakaria Adam Jigirya

 

Dan Majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji Hon Abdulmumin Jibrin Kofa PhD, ya kafa tarihin gabatar da kudurori har guda 15 a zauren majalisar, kuma tuni dukkansu suka tsallake matakin karatu na farko a cikin mako ɗaya.

Daga cikin ƙudurorin har da na kafa Jami’ar Kasuwanci ta Kofa, Bebeji, Kano, wanda shi tuni ya tsallake matakin karatu na biyu. Sannan akwai wasu ƙudurorin da suka shafi yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, bunƙasa harkokin zuba jari da kasuwanci, bayar da ilimin kyauta da kuma ilimin gaba da sakandare da dai sauransu.

Ɗan Majalisar dai ya ɗauki lokaci sosai wajen yin nazari mai zurfi kan buƙatun mutanen mazaɓarsa, kafin ya gabatar da ƙudurorin a majalisa.

InShot 20250115 195118875
Talla

“Jami’ar Kasuwancin za ta kasance irinta ta farko wajen horar da jajirtattun matasanmu, domin su kasance maso dogaro da kai a harkar kasuwanci, ta yadda za su yi shi bisa ilimi sannan su yi gogayya da takwarorinsu a kasuwannin ciki da wajen Najeriya.

Kano dai ita ce babbar cibiyar kasuwanci a Najeriya, inda take kafaɗa da kafaɗa da Jihar Legas. Saboda haka, amfanin wannan jami’ar ga mazaɓar Kiru/Bebeji, Jihar Kano da Najeriya baki ɗaya, ba zai misaltu ba.

Matsalar tsaro: Gwamna Kano ya kafa Kwamitin karta-kwana

Ga Wasu Daga Cikin Faidojin da za a Samu Idan jami’ar ta tabbata

Da yake gabatar da kudirin a zauren majalisar Kofa, ya ce ya idan aka samar da jami’ar za ta taimaka sosai wajen samawa matasa aikin yi, musamman idan aka yi la’akari da kudirin shugaban kasa Bola Tinubu na magance zaman kashe wando a tsakanin matasa.

Idan har wannan jami’a ta tabbata ilimi zai kara samuwa a cikin al’ummar jihar Kano da arewacin Nigeria, musamman al’ummar da suke yankin kananan hukumomin Kiru Bebeji, Madobi, Karaye Kura da Rano da sauran kananan hukumomin da ke makwaftaka da Bebeji.

Kungiyar ma’aikatan hukumar kula da kananan hukumomin Nigeria ta yabawa Gwamnan Kano

Wata dama ta biyo ita ce yadda za a rage yawan matasan da ba su da aikin yi a yankin da jihar Kano baki daya. Kowa ya sani cewa aikin gwamnati ba samuwa yake ba , don haka duk dalibin da ya kammala jami’ar zai za mo kai tsaye ya sami sana’ar da zai dogara da kansa.

Dama ta uku ita ce al’umma da yawa za su sami Aikin yi a cikin jami’ar, domin dole ne kananan ma’aikata da za a dauka a jami’ar su zamo yan asalin inda aka samar da jami’ar ne.

Babu shakka idan Wannan jami’a ta tabbata, dalibai da yawa za su rika samun gurbin karatu duk shekara, sabanin yadda a yanzu wasu ke rasa gurbin karatu saboda karancin jami’o’in gwamnati wadanda sune ya’yan talakawa ke samun damar zuwa.

A kwai bukatar a taya Abdulmumin Jibrin Kofa da add’o’in Allah ya ba shi nasara wannan jami’a ta tabbata don samar da cigaba mai yawa ga al’ummarsa.

Abdulmumin Jibrin Kofa da ya ce zai ci gaba da yin duk ƙoƙarinsa wajen kawo romon Dimokuraɗiyya ga yankin Kiru/Bebeji, Kano da Najeriya baki ɗaya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...