Ba wani maniyaci dan Nigeria da zai rasa Aikin Hajjin bana – Shugaban NAHCON

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya ƙaryata rahoton cewa ya soke yarjejeniyar hidimomin alhazai da wasu kamfanoni na Saudi Arebiya domin aikin Hajjin bana.

Rahotanni sun bayyana cewa Ƙungiyar shugabannin hukumomin din daɗin Alhazai ta Jihohi ta zargi Shugaban na NAHCON da soke kwangilar wani kamfani da ke Saudiyya kai tsaye, wanda hakan na iya kawo cikas ga Hajjin 2025.

Ƙungiyar, ta bakin Sakatarenta, Alhaji Abubakar Salihu, wanda shi ne Babban Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Adamawa, ta yi gargadin cewa soke yarjejeniyar da aka yi da kamfanin Mashariq Al-Dhahabiah na Saudiyya na iya hana Alhazan Najeriya samun takardun izinin shiga Saudiyya don Hajjin 2025.

InShot 20250115 195118875
Talla

Sai dai bangaren shugaban na NAHCON ya musanta zargin, a martanin da masu tallafawa wajen yada labarai na hukumar NAHCON suka fitar.

A cewarsu, zargin bai da tushe balle makama kuma an yi hakan ne don kawo cikas ga shirye shiryen aikin Hajjin na Bana.

Atiku Abubakar ya yi ganawar sirri da Obasanjo

Shi ma anasa martanin, Shugaban na NAHCON ya bayyana cewa: “Gwamnatin Saudiyya ce da kanta ta soke kwangilar a karon farko, daga bisani ta sake amincewa da ita sannan ta sake soke ta karo na biyu. Don haka, babu hannunsa a cikin soke yarjejeniyar.

Ya ƙara da cewa, “Saboda wannan matsala, na zo Saudiyya don tabbatar da an yi abin da ya dace bisa doka da gaskiya, kuma ina tabbatar muku cewa babu Alhaji da zai rasa damar zuwa Hajjin bana.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...