Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar Kano (SSG).
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24 a ranar Asabar.
![Talla InShot 20250115 195118875](https://kadaura24.com/wp-content/uploads/2025/02/InShot_20250115_195118875-300x298.png)
Nadin Ibrahim zai fara aiki daga ranar Litinin 10 ga Fabrairu, 2025.
Sanarwar ta ce, an zabi Ibrahim ne bisa gogewar da yake da ita, wanda ake sa ran zai yi amfani da ita wajen inganta harkokin gwamnatin jihar Kano.
Gwamnatin Kano za ta tallafawa matasa 3000 da wata kungiya ke koyawa sana’o’i a Kano – Sani Danja
Umar Farouk Ibrahim da ta kwashe sama da shekaru talatin yana aikin gwamnati , don haka ake fatan zai kawo cigaba sosai a sha’anin tafiyar da harkokin aikin gwamnati.