Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-naden mukamai

Date:

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin shugabannin hukumar kare hakkin mai saye da mai sayarwa ta jihar Kano domin tabbatar da adalci da kare hakkin masu sayen kaya a dukkanin kasuwannin jihar Kano.

Hakan na kunshe cikin wata samarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24.

InShot 20250115 195118875
Talla

Kunshin wakilan hukumar sun hada masana da kwararru da jami’an gwamnati da kuma wakilcin yan kasuwa domin tabbatar da daidaito da adalci a gudanarwar hukumar.

Sanarwar ta bayyana Dr. Umar Garba Haruna a matsayin shugaba yayin da Alhaji Zangina Jafaru zai kasance a matsayin babban sakataren hukumar.

Aiyuka 5 da Gwamnan Kano ya yi alkawarin yi, bayan dakatar da rusau a Rimin Zakara

Sauran wakilan hukumar sun hada da Alhaji Ibrahim Ahmad Gama daga Kano ta tsakiya da Hajiya Safiya Umar Bichi daga Kano ta Arewa da Alhaji Hussaini Bello Gidado daga Kano ta Kudu.

Kazalika kunshin wakilan hukumar ya hada da Alhaji Munzali Abubakar daga Kasuwar Kantin kwari da Alhaji Muhammad Adakawa daga kwanar singa da Alhaji Ahmad Isa Chedi daga Kasuwar Dawanau da Alhaji Sani Gambon daga Sabon gari.

Sauran wakilan hukumar sun kunshi jami’ai daga ma’aikatar Sharia da ta lafiya da ta Mahalli da kuma ma’aikatar sufuri.

Sanarwar ta bukaci sabbin wakilan hukumar da su fara aiki nan take domin kawo karshen korafe-korafe tsakanin mai saye da mai sayarwa da kuma tsaftace al’amuran Kasuwanci a jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...