Gwamnatin Kano Ta Kammala Aikin Gina Mayanka ta Naira Biliyan 1.5

Date:

Daga Zakaria Adam Jigirya

 

 

Gwamnatin jihar Kano ta karkashin Shirin bunkasa noma da kiwo na jihar (KSADP) ta kammala aikin gina mahauta guda 20 a fadin jihar, wanda aka kashe naira biliyan 1.5. Wajen gina su.

An dai yi mayankar ne a kananan hukumomin Dawakin Tofa, Kunchi, Bichi, Gezawa, Tudun Wada, Kura, Rano, Bebeji, Wudil, Doguwa, Gabasawa, Gaya, Sumaila, Takai, Kabo, Shanono, Karaye, Kiru, da Gwarzo.

KSADP, wanda Bankin Raya Musulunci (IsDB) da Asusun bunkasa Rayuwar al’umma (LLF) su ke tallafawa, da kuma gwamnatin jihar, na da burin tabbatar da ingantacciyar lafiyar nama da rage yaduwar cututtuka da suka shafi dabbobi.

InShot 20250115 195118875
Talla

Ko’odinetan shirin na Jihar Kano Ibrahim Garba Muhammad ne ya bayyana hakan a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki a dakin taro na Global Luxury Suites da ke Kano, inda suka tattauna dabarun gudanar da ingantaccen tsari, mai dorewa, da kuma kiyaye lafiyar al’umma a mahauta.

“Manufar wannan tsarin ita ce tabbatar da lafiyar nama, lura da cututtukan dabbobi, da kuma kula da dakile yaduwar cututtukan dabbobi ga al’umma,” in ji Muhammad. Ya kuma jaddada muhimmancin yin amfani da kayayyakin da aka sanya a wuraren don gudun ka da a sace su.

An dakatar da Shugaba da Sakataren kungiyar APC X Eagle forum

Sani Rabi’u Muhammad babban mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin mayanka, ya jaddada cewa an kira taron ne domin tattauna hanyoyin yadda za’a kare kayan da aka sanya don gudun kada batagari su sace su.

Ya kara da cewa, “An mayar da hankali ne wajen tabbatar da nasarar gudanar da ayyukan wadannan mayanka”

Sarkin Fawar Kano, Alhaji Isyaku Alin Muri, ya godewa gwamnatin jihar Kano, da ISDB, da LLF bisa wannan gagarumin aikin. Ya kuma bayyana mayankar a matsayin wani gagarumin ci gaba da aka samu wajen kula da lafiyar nama a Kano.

Ma’aikatun noma na cikin gida an dora musu alhakin hada kai da masu ruwa da tsaki domin ganin an samu nasarar aiwatar da aikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...

Mun gano yadda yan Bauchi ke mamaye dazukan Kano – Gwamnatin Kano

Daga Nazifi Dukawa     Gwamnatin jihar Kano ta ce ta gano...

An dakatar da Shugaba da Sakataren kungiyar APC X Eagle forum

Kwamitin zartarwa na kungiyar APC X Eagle forum ya...

Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata

Daga Isa Ahmad Getso   Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja'atu Muhammad...