Kwamitin zartarwa na kungiyar APC X Eagle forum ya ce ya dakatar da shugaban kungiyar Ahmad Gogel da sakataren kungiyar M I Tudun Wada bisa zarginsu da rashin iya jagoranci da zubar da kimar ofisoshinsu.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka aikowa Kadaura24, mai dauke da sa hannun Najib Bala Salihu (Dawaki),Kabir Waya da Mukhtar Kabir Maitama da Farouk DanBatta.
“Muna amfani da wannan dama domin sanar da ya’yan Wannan kungiya da jagororin Jam’iyyar APC da ma dukkanin al’umma cewa mun dakatar da shugaba da sakatare na wannan kungiyar don haka kar kowa yayi mu’amala da su a matsayin Shugabannin kungiyar APC X Eagle Forum”.
Sanarwar ta ce ba a dauki wannan matakin ba sai da aka gudanar da bincike tare da tuntuba wadanda suka dace sannan aka yankin wannan matakin na dakatar da su.
“Za mu nada wadanda za su yi ke matsayin shugaba da sakatare na kungiyar nan gaba kadan, domin cigaba da aiwatar da aiyukan kungiyar da kuma kare martaba da kimar jam’iyyar ta APC da kuma jagororinmu”. A cewar sanarwar
Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata
Sanarwar ta kara da cewa” Mun gamsu da salon jagorancin shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje, sannan muna amfani da wannan dama wajen kara jaddada mubaya’armu ga mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, kuma muna yi masa fatan cikin da yin mulkinsa cikin koshin lafiya”.
“Muna kara jaddada goyon bayanmu ga Jam’iyyar APC da Jagoranta kuma za mu cigaba da yi musu biyayya a kokarinsu na ciyar da jam’iyyar gaba da kuma hada kan ya’yan jam’iyyar.