Daga Isa Ahmad Getso
Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja’atu Muhammad ta ce har yanzu tana nan akan bakarta kan maganar da ta fada akan mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro Nuhu Ribado.
Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito cewa Nuhu Ribado ya yi barazanar maka Hajiya Naja’atu Muhammad a kotu matukar bata janye kalaman da tayi a akansa ba.
Hajiya Naja’atu Muhammad ta bayyana hakan ne yayin wata hira da ta yi da gidan Rediyon Premier dake Kano.
“Ina nan akan bakara ba zan janye kalami na ba, ballantana na ba shi hakuri, idan ya so ya kaini Kotun koli”. Inji ta
Ta ce maganar da ta fada ba karya ba ce, sai dai idan shi ne ya yiwa mutane karya lokacin da ya ke a matsayin shugaban hukumar EFCC.
Idan za’a iya tunawa dai Hajiya Naja’atu Muhammad ta ce a lokacin da Nuhu Ribado yake a matsayin shugaban hukumar EFCC ya ce Tinubu cikakken dan cin hanci da rashawa ne.